Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun cafke Fati Cele bayan rasuwar saurayinta a gidanta

’Yan sanda sun cafke Fati Cele bayan rasuwar saurayinta a gidanta

Ana gudanar da bincike bayan mutuwar wani da ake zargin saurayin Fati Cele ne a Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tsare fitacciyar ’yar TikTok, Fati Cele, bayan mutuwar wani matashi da ake zargin saurayinta ne a gidanta.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwar murya da ya aikewa jaridar Punch a ranar Asabar.

Sai dai ya ce ba zai yi karin bayani kan lamarin ba a halin yanzu, domin ana ci gaba da gudanar da bincike.

Fati Cele, wadda ke zaune a unguwar Dan Bare a Kano kuma ’yar asalin Jihar Borno ce, na daga cikin fitattun masu amfani da TikTok.

Wani shaidu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mamacin ya fito daga gidan yana neman agaji bayan da wata gobara ta tashi a cikin gidan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments