Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Zamfara ya yabawa sojoji kan kwato daruruwan dabbobi daga wajen ’yan...

Gwamnan Zamfara ya yabawa sojoji kan kwato daruruwan dabbobi daga wajen ’yan bindiga

Sojoji sun kwato shanu 329 da tumaki 175 daga hannun ’yan bindiga a Zamfara.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba da jajircewar dakarun Sojin Nijeriya wajen ci gaba da gudanar da hare-hare kan masu aikata laifuka a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya jinjinawa sojojin bayan sun kwato shanu 329 da tumaki 175 daga hannun ’yan bindiga a dajin Gambanda da ke karamar hukumar Gummi.

Hakazalika, ya yaba da gudunmawar rundunar ’yan sandan jihar, yana mai cewa kokarinsu na taimakawa wajen inganta zaman lafiya da tsaro a fadin Zamfara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments