Wasu sojojin Najeriya sun rasa rayukansu bayan wata na’urar fashewa da ake zargin ƴan ta’adda ne suka dasa ta tashi a wani yanki da ke Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun ke kan hanyarsu ta amsa kiran gaggawa daga al’ummar wani yanki da suka nemi taimakon jami’an tsaro.
Har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan adadin waɗanda abin ya shafa ba, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike domin gano musabbabin harin da kuma waɗanda ke da hannu a cikinsa.