Kayode Egbetokun ya buƙaci jami’an rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano da su ƙara zage damtse wajen yaƙi da miyagun ayyuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
Sufeto Janar ɗin ya jaddada cewa ɗaukar matakan gaggawa da saurin mayar da martani ga barazanar tsaro na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
An bayyana wannan saƙo ne ta bakin Mataimakin Sufeto Janar mai kula da harkokin kuɗi da gudanarwa, Suleiman Abdul, yayin wani taron horaswa da nazarin dabarun tsaro da aka gudanar a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano da ke Bompai.
Ya kuma ƙarfafa jami’an da su ci gaba da aiki da ƙwarewa, jajircewa da haɗin kai domin dakile ayyukan masu aikata laifuka da tabbatar da tsaron al’umma.