Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotun Birtaniya ta wanke tsohuwar minista Diezani daga zargin cin hanci

Kotun Birtaniya ta wanke tsohuwar minista Diezani daga zargin cin hanci

Wata kotun sauraron manyan laifuka da ke Southwark a birnin Landan ta wanke tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Wata kotun sauraron manyan laifuka da ke Southwark a birnin Landan ta wanke tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Alkalai masu yanke hukunci sun yanke hukuncin ne a ranar Laraba bayan shafe sama da sa’o’i 46 suna nazari kan shari’ar. A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, hukuncin ya kasance babban koma baya ga hukumomin Birtaniya da ke tuhumar ta.

Diezani, mai shekaru 65, wadda ta riƙe muƙamin ministar man fetur tsakanin 2010 da 2015 a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta fuskanci tuhume-tuhume guda biyar na karɓar cin hanci da kuma laifin haɗa baki domin aikata cin hanci.

Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa wasu jiga-jigan masana’antar mai da iskar gas sun samar mata da rayuwar alfarma a Landan domin samun kwangiloli masu tsoka a Najeriya.

Sai dai Diezani ta musanta zarge-zargen tun daga farko, tana mai cewa ba ta da ikon kai tsaye wajen bayar da kwangiloli. Lauyoyinta sun bayyana cewa kuɗaɗen da ake magana a kai ko dai gwamnatin Najeriya ce ta biya su don ayyukan hukuma ko kuma ita kanta ta biya kuɗin abubuwan da suka shafi rayuwarta.

Bayan an wanke ta, lauyanta ya ce Diezani ta nuna godiya ga alkalan kotun, yana mai cewa ta sha wahala tsawon shekaru 11 saboda rabuwa da iyalanta sakamakon shari’ar.

Sanarwar ta ƙara da cewa yanzu an ba ta damar komawa rayuwarta ta kashin kai da ta jama’a bayan an wanke sunanta daga zarge-zargen da ake yi mata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments