Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta karyata rahotannin sabbin haraji kan mai da sadarwa

Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin sabbin haraji kan mai da sadarwa

Rahotannin sun fara yaɗuwa ne bayan wallafar rahoton tattalin arzikin Najeriya na Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar ƙarin haraji a ƙasar.

Rahotannin sun fara yaɗuwa ne bayan wallafar rahoton tattalin arzikin Najeriya na Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar ƙarin haraji a ƙasar.

Sai dai Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana cewa shawarwarin da IMF ke bayarwa ra’ayoyi ne kawai da gwamnati za ta iya yin nazari a kansu, kuma ba su zama doka ko manufofin gwamnati kai tsaye ba.

Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa rangwamen harajin VAT kan kayayyakin man fetur yana nan daram, yayin da harajin sadarwa “telecom excise duty” da aka ƙaddamar kafin shekarar 2023 an riga an soke shi a ƙarƙashin sabbin dokokin haraji.

Haka kuma ta ce duk wani mataki kan ƙarin kuɗi a kan man fetur ba zai fara aiki ba sai an bi hanyoyin doka da suka haɗa da amincewar minista da wallafawa a jaridar gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa a halin yanzu hankalinta na kan bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa tattara kuɗaɗen shiga, jawo hannun jari da samar da ayyukan yi, maimakon ɗora wa al’umma sabon nauyin haraji.

Ta ƙara da cewa duk wani sabon tsarin haraji a nan gaba za a sanar da shi ne a hukumance tare da aiwatar da shi bisa tanadin doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments