Jagoran jam’iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, ya ƙaddamar da wata sabuwar doka da ta tilasta wa duk masu neman takara a ƙarƙashin jam’iyyar yin alƙawarin ci gaba da kasancewa a cikinta bayan sun lashe zaɓe.
A ƙarƙashin dokar, duk ’yan takara za su sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi cewa duk wanda ya sauya sheƙa bayan samun nasara a zaɓe zai rasa kujerarsa.
Matakin ya shafi kowane ɗan takara na jam’iyyar, ciki har da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da NDC ke ƙoƙarin hana sauya sheƙar ’yan siyasa tare da ƙarfafa haɗin kai gabanin zaɓen 2027.