Majalisar Dattawa ta Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da wani zaman gaggawa a ranar 23 ga watan Yuni domin nazari kan wasu manyan batutuwan da suka shafi ƙasa, musamman matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya.
A wata sanarwa da Magatakardar Majalisar Dattawa, Emmanuel Odo, ya fitar, an bayyana cewa za a dakatar da hutun da sanatoci ke yi domin ba da damar gudanar da zaman na musamman.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sakamakon muhimmancin batutuwan da ke buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Za a gudanar da zaman ne da misalin ƙarfe 11 na safe a zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja.
Ana sa ran sanatoci za su tattauna matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren ƴan bindiga, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, da sauran barazanar tsaro, tare da lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin.