Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniWasan Najeriya da Portugal: Wace kasa ku ke ganin za ta yi...

Wasan Najeriya da Portugal: Wace kasa ku ke ganin za ta yi nasara?

Tawagar Portugal za ta kammala shirye-shiryenta na gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 da wasan sada zumunta da Najeriya a ranar Laraba, kafin ta nufi sansaninta da ke jihar Florida a Amurka.

Super Eagles za ta shiga wasan da kwarin gwiwarta bayan da ta shafe wasanni biyar a jere ba tare da dandana kaye ba.

A wasanta na baya-bayan nan, Najeriya ta tashi canjaras da Poland da ci 2-2, inda Terem Moffi da Paul Onuachu suka zura kwallayen da suka taimaka wa kungiyar ta samu sakamako mai kyau.

Kafin wannan wasa, Super Eagles ta samu nasarori masu kayatarwa a wasannin sada zumunta, inda ta lallasa Jamaica da ci 3-0 sannan ta doke Zimbabwe da ci 2-0.

Ana sa ran wasan da Portugal zai kasance mai zafi, musamman ganin cewa kungiyar Turai na dauke da manyan taurari ciki har da Cristiano Ronaldo.

Magoya baya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan wanda zai yi fice a wasan, yayin da wasu ke sa ran ganin Moffi, Onuachu da sauran ’yan wasan Super Eagles sun ci gaba da nuna bajintar da suke yi a baya-bayan nan.

Shin Najeriya za ta ci gaba da jerin wasannin da ba a doke ta ba, ko kuwa Portugal za ta nuna karfinta kafin fara gasar kofin duniya?

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments