Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya yi karin haske kan ziyarar da ya kai birnin Ibadan a jihar Oyo a karshen shekarar da ta gabata, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan ziyarar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 9 ga Yunin 2026, Sheikh Gumi ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne a matsayin wakilin gamayyar malaman Musulunci na Arewa.
Malamin ya ce babu wani dan Najeriya da zai hana shi ziyartar kowace jiha a fadin kasar nan, yana mai jaddada cewa Najeriya kasa ce ta kowa da kowa.
Ya kuma musanta rahotannin da ke cewa wasu kungiyoyin Musulmi daga yankin Kudu maso Yamma ne suka gayyace shi zuwa Ibadan, yana mai cewa babu wata kungiya ko mutum daga yankin da ya gayyace shi domin wannan ziyara.
Bayanin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan wasu zarge-zargen da suka shafi masu garkuwa da mutane a jihar Oyo.
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, shugabar makarantar Community High School da ke Esiele, Misis Rachael Alamu, wadda aka sace a baya, ta musanta ikirarin cewa masu garkuwar sun bukaci a kafa shari’ar Musulunci a jihar ko kuma a biya kudin fansar naira biliyan daya.
Ta bayyana cewa abin da masu garkuwar suka nema shi ne a sako wasu abokan huldarsu da ke tsare kawai.