Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da mata huɗu, ciki har da mai juna biyu, a wani hari da suka kai da daddare a ƙauyen Maikadauri da ke ƙaramar hukumar Kontagora a jihar Neja a ranar Litinin.
Majiyoyi da suka nemi a sakaya sunayensu sun shaida wa Daily Trust cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin harin.
Sun kuma bayyana cewa wani ɗan sa-kai mai suna Amos, wanda ya yi yunƙurin kai wa mazauna yankin ɗauki lokacin harin, ya samu harbin bindiga a ƙafarsa.
Wani mazaunin Kontagora, Habibu Mohammed, ya ce hare-haren da ake kai wa al’ummomin da ke bayan garin na ci gaba da faruwa duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar rashin tsaro da ke ƙara kamari a yankin.
Wannan hari ya biyo bayan kashe wasu matasa biyu, Sidiq Musa da Bashar Bisalla, da wasu masu ɗauke da makamai suka harbe yayin da suke tattara itacen girki a dajin Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu.
Mazauna yankin sun ce aƙalla matasa bakwai ne aka kashe a wannan daji cikin kwanaki 110 da suka gabata yayin da suke neman itacen girki.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, bai yi nasara ba, domin ba a samu shigan wayarsa ba kuma bai amsa saƙon kar-ta-kwana da aka tura masa ba.