Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya samu tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, da laifuka 12 da suka shafi damfara da halasta kuɗaɗen haram da Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar a kansa.
Ko da yake Mamman bai halarci kotun ba, alƙalin ya ce an tabbatar da cewa aƙalla Naira biliyan 22 an wawure ta hannunsa tare da wasu abokan hulɗarsa.
“Masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa an karkatar da aƙalla Naira biliyan 22 ta hannun wanda ake ƙara da abokan aikinsa. Wannan ya isa ya tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da shi. Saboda haka, kotu ta same shi da laifi a tuhume na farko,” in ji alƙalin.
Haka kuma, kotun ta ce ɓangaren kariya bai gabatar da hujja mai ƙarfi da za ta ƙaryata shaidun da masu gabatar da ƙara suka kawo ba.