Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiƊan NYSC ya rasa ransa a bakin tekun jihar Bayelsa

Ɗan NYSC ya rasa ransa a bakin tekun jihar Bayelsa

Wani matashin mai hidimar ƙasa (NYSC), Ajetunmobi Sunday Dayo ya rasa ransa bayan nutsewa a rairayin bakin teku na Akassa da ke jihar Bayelsa yayin da yake iyo tare da abokan aikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya je rairayin bakin teku na Okumbiribeleu da ke al’ummar Akassa a ƙaramar hukumar Brass ranar Asabar domin yawon shakatawa tare da sauran masu yi wa ƙasa hidima lokacin da lamarin ya faru.

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa Dayo yana iyo tare da abokan aikinsa kafin daga bisani ya ɓace.

Bayan sun lura ba sa ganin sa, abokan nasa suka fara nemansa tare da sanar da jami’an yankin.

Majiyar ta ce masu ruwa da tsaki da masu nutso na yankin sun fara aikin ceto bayan an tada ƙararrawa, amma ba a same shi ba.

An gano gawarsa ne ranar Litinin bayan ruwa ya fitar da ita zuwa bakin teku.

An ce jami’an NYSC a Jihar Bayelsa sun binne shi bayan samun amincewar iyayensa.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin yana aiki ne a makarantar Community Secondary School Kongho da ke Akassa kafin faruwar lamarin.

Shi da sauran abokansa sun tashi daga masaukinsu da ke Tobukiri zuwa rairayin bakin teku na Okumbiribeleu domin yawon buɗe ido kafin hatsarin ya auku.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta NYSC a Bayelsa, Misis Yvonne Halliday-Urie, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana shi a matsayin abin takaici.

Ta ce:
“Labarin gaskiya ne kuma abin baƙin ciki ne. An binne shi jiya a Yenagoa. NYSC ta gudanar da jana’izarsa bisa bukatar iyayensa.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bayelsa State, DSP Musa Mohammed, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar hatsarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments