Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGwamnatin Kano ta musanta rahoton kisan mutane biyar a ranar rantsar da...

Gwamnatin Kano ta musanta rahoton kisan mutane biyar a ranar rantsar da Murtala Sule Garo

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ba a samu kisan mutane biyar ba a lokacin rantsar da Murtala Garo.

Gwamnatin jihar Kano ta nesanta kanta da zargin mutuwar mutane biyar yayin bikin rantsar da Murtala Garo.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.

Sanarwar tace binciken da gwamnati da jami’an tsaro suka gudanar bai tabbatar da faruwar lamarin ba, sakamakon gaza samun rahoto a hukumance.

Sanarwar ta bayyana cewa rikicin da ake zargin wasu ‘yan daba sun yi, bai faru a kusa da gidan gwamnati ba, saboda haka bai kamata a danganta shi da bikin gwamnatin jihar ba.

Gwamnatin ta kuma nuna takaicinta kan yadda kungiyar Amnesty International ta wallafa rahoton ba tare da tantancewa daga jami’an tsaro ko hukumomin gwamnati ba, inda ta zargi kungiyar da dogara da bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments