Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƘungiyar ISIS ta ɗauki nauyin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane...

Ƙungiyar ISIS ta ɗauki nauyin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 30 a Adamawa

Rahotanni sun nuna cewa ISIS ta ɗauki alhakin harin da ya hallaka aƙalla mutum 30 a Adamawa

Wasu ƴan bindiga sun hallaka aƙalla mutane ashirin da tara a jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga wani filin wasan ƙwallon ƙafa ne inda jama’a ke taruwa, kana suka buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi.

Ofishin gwamnan jihar ya ce maharan sun shafe sa’o’i da dama suna harbin jama’a da ƙona gidaje, da babura da wuraren ibada.

A shekarun baya-bayan nan, yankin ya sha fama da hare-hare daga kungiyoyin ‘yan daba na cikin gida da kuma masu alaka da ISIS.

Wata sanarwa da kungiyar ta ISIS ta wallafa a shafinta, ta dauki alhakin kai harin.

Rahotanni sun nuna cewa an tura jami’an soji da ƴan sanda zuwa yankin domin daƙile yiwuwar sake kai wani harin.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments