Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAPC ta sake tsara jadawalin zaɓen ta na cikin gida

APC ta sake tsara jadawalin zaɓen ta na cikin gida

Miƙa fom da aka cika zai ƙare a ranar 4 ga Mayu, 2026.

APC ta fitar da sabon jadawalin ayyuka na zaɓen 2027, inda ta gyara lokutan tantance ‘yan takara, zaɓen fidda gwani, daukaka ƙara, da sauran matakan cikin gida na jam’iyya.

Haka kuma ta bayyana asusun banki da za a biya kuɗin fom ɗin sha’awar takara da na tsayawa takara.

Sanarwar, wadda aka fitar daga hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, ta samu sa hannun Sakataren Tsare-tsare na ƙasa, Sulaiman Muhammad Argungu, tare da tabbatarwa daga Kakakin jam’iyyar, Felix Morka.

Jam’iyyar ta ce ta yi hakan ne bisa tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka gyara, dokar zaɓe ta 2026, da kuma jadawalin INEC na zaɓen 2027.

A cewar jadawalin, sayar da fom zai gudana daga 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026.

Miƙa fom da aka cika zai ƙare a ranar 4 ga Mayu, 2026

Za a fara tantance ‘yan takara daga 6 zuwa 9 ga Mayu, 2026, wanda zai shafi ‘yan takarar majalisar jiha, majalisar wakilai, majalisar dattawa, gwamnoni da shugaban ƙasa.

Za a gudanar da sauraron ƙorafe-ƙorafe na majalisar jiha da ta wakilai daga 12 zuwa 13 ga Mayu, 2026.

Zaɓen fidda gwani zai fara daga 15 ga Mayu, 2026 da majalisar wakilai, sannan majalisar dattawa, majalisun jihohi, gwamnoni da shugaban ƙasa, inda zai ƙare a ranar 23 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta kuma fitar da kuɗin fom kamar haka:
Majalisar Jiha N1,000,000, kuɗin na gani ina so, sai kuma N5,000,000 na tsayawa takara.

Majalisar Wakilai: N1,000,000 da N9,000,000
Majalisar Dattawa: N3,000,000 da N17,000,000
Gwamna: N10,000,000 da N40,000,000
Shugaban ƙasa: N30,000,000 da N70,000,000

APC ta ce mata, matasa da masu nakasa za su biya kuɗin fom na sha’awa kawai da rabin kuɗin fom na tsayawa takara.

Ta kuma umarci cewa duk kuɗaɗen a biya su kai tsaye cikin asusun bankin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa wannan sabon jadawalin wani ɓangare ne na shirye-shiryenta domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin gida cikin tsari da inganci yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments