Wani babban jami’i a kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa ana ba da wani nau’in tallafi a kan fetur da dizal da ake sayarwa a kasuwar Najeriya.
A cewarsa, farashin fetur da matatar ke sayarwa a kusan Naira 1,200 a kowace lita yana ƙasa da ainihin farashin kasuwa, musamman duba da yadda farashin danyen mai ya tashi sakamakon rikicin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran.
Rahoton ya nuna cewa faruwar rikicin Gabas ta Tsakiya ya sa farashin mai ya haura daga kusan Dala 66 a kowace ganga zuwa sama da Dala 100.
Mataimakin shugaban ƙungiyar masu jiragen sama ta Najeriya, Allen Onyema, ya bayyana cewa farashin man jirgin sama ya tashi sosai—daga kusan Naira 900 zuwa tsakanin Naira 2,700 zuwa 2,900 a kowace lita, yayin da wasu ke sayar da shi har Naira 3,500.
Jami’in Dangote ya ce kamfanin na ƙoƙarin rage farashin fetur da dizal domin sauƙaƙa wa jama’a, amma ba zai iya yin hakan ga dukkan nau’ikan mai ba.
Ya ƙara da cewa man jiragen sama ana sayar da shi ne a farashin kasuwa, ba tare da wani tallafi ba. Ya danganta tashin farashin mai da hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya.