Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaDamuwar da Peter Obi ke nunawa game da Arewacin Najeriya yaudara ce...

Damuwar da Peter Obi ke nunawa game da Arewacin Najeriya yaudara ce da munafurci – Sowore

Sowore ya zargi Peter Obi da nuna damuwa ta ƙarya kan matsalolin Arewa.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya soki Peter Obi kan zargin yin munafunci sakamakon kalaman yabo da ya ke yi wa yankin Arewacin Najeriya.

Peter Obi, wanda ya kasance jigon jam’iyyar ADC ya bayyana cewa zai ba wa cigaban Arewacin Najeriya fifiko, inda ya siffanta yankin a matsayin babbar kadara ga ƙasar nan.

Da yake mayar da martani, Sowore ya tunatar da ‘yan Arewacin Najeriya wani tarihi da ya shuɗe.

Ya bayyana cewa a lokacin da Peter Obi yake matsayin Gwamnan Jihar Anambra, ya taɓa ba da umarnin a kamo ‘yan Arewa mazauna jihar sannan aka tisa keyarsu aka mayar da su yankunansu na asali.

A cewar Sowore, hakan na nuna cewa yabon da Obi ke yi wa Arewa a yanzu na neman ƙuri’a ne kawai ba don yana ƙaunarsu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments