Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin karɓar sabbin rancen kuɗaɗe daga ƙasashen waje da suka haura dala biliyan 6, matakin da ake sa ran zai kai jimillar bashin Najeriya sama da naira tiriliyan 195.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da (IMF) ta bayyana damuwa kan yawaitar haɗarin bashin da ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ke fuskanta.
A cikin wasiƙu biyu daban-daban da ya aikewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, shugaban ƙasa ya bayyana cewa za a yi amfani da sabbin rancen wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa, biyan wasu basussuka, da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa.