Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEl-Rufai ya sake bayyana a kotu kan neman beli

El-Rufai ya sake bayyana a kotu kan neman beli

El-Rufai ya sake bayyana a kotu yayin sauraron bukatar beli

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake bayyana a gaban Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda ake sa ran sauraron bukatarsa ta neman beli.

A makon da ya gabata ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (ICPC) ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Rilwan M. Aikawa bisa tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin jama’a da kuma safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.

An gabatar da tsohon gwamnan a gaban kotu bayan ya shafe sama da wata guda a tsare.

Kotun dai ta sanya ranar 31 ga Maris, 2026 domin sauraron wasu bukatu da ke gaban ta, ciki har da na neman beli.

Sai dai a ranar 31 ga Maris, an dage shari’ar zuwa ranar 1 ga Afrilu, 2026, bayan masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa sun shigar da martanin su ne a wannan rana.

Sai dai Jigon jam’iyyar ADC ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, inda ya bayyana shari’ar a matsayin farautar siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments