Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tabbatar da cewa za a yi zaben cike gurbi a wasu kujeru uku a majalisar bayan rasuwar sanatocin da ke wakiltar su.
Kujerun sun hada da shiyyar Enugu ta Arewa, Nasarawa ta Arewa da Santoriyar Kudancin Rivers .
Ya bayyana hakan ne a zaman majalisa, inda ya ce matakin ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin kasa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Akpabio ya kara da cewa Hukumar Zabe ta Kasa, (INEC), za ta shirya zabukan cike gurbin domin maye gurbin sanatocin da suka rasu.