Rundunar sojoji ta damƙe mutane 58 kan zargin shiga harkar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
An kama waɗanda ake zargin ne a wani wajen haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba a Ososo, ƙaramar hukumar Akoko-Edo.
A cewar Kyaftin Kennedy Anyanwu, an kama waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 1 na rana a ranar 28 ga watan Maris, 2026, yayin wani sintiri da aka yi bisa sahihan bayanai.
Ya ce wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuka a Jihar Edo.
An kama su kuma an miƙa su ga ‘yansanda a Okpella domin ci gaba da bincike.