Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce umarnin ya fito ne ta hannun Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.
Sanarwar ta jaddada cewa matakin ya yi daidai da sashe na 88 karamin layi na 1 na dokar zabe ta 2026, wanda ya kayyade yadda jami’an gwamnati ke shiga harkokin siyasa.
Takardar Sanarwar ta rawaito Sakataren gwamnatin na cewa e an dauki matakin ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma samar da damar fafatawa ga dukkan masu neman mukamai.
Sanarwar dai na umartar dukkan masu ruwa da tsakin da abun ya shafa, da su tabbatar da bin umarnin, inda aka bukaci masu niyyar tsayawa takarar su yi murabus kafin ranar 31 ga Maris, 2026.