Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaDauda Lawal shi ne ɗan takarar Gwamnan APC a Zamfara – Bello...

Dauda Lawal shi ne ɗan takarar Gwamnan APC a Zamfara – Bello Matawalle

Bello Matawalle ya bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayi dan takarar Gwamnan APC a zamfara

Ƙaramin Ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba zai nemi tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027 ba.

Ya kuma bayyana cewa zai goyi bayan gwamna mai ci, Dauda Lawal.

Matawalle ya faɗi haka ne a birnin Gusau, lokacin wani babban taron liyafa da aka shirya domin karɓar Gwamna Lawal zuwa jam’iyyar APC.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya jagoranci taron da aka yi a filin Trade Fair Complex a ranar Talata, 24 ga Maris, 2026.

Ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa Gwamna Dauda Lawal, yana mai ƙara da cewa yana da yaƙinin Zamfara za ta samu ci gaba idan suka haɗa kai domin yi wa al’umma aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments