Gwamnatin Tarayya ta nemi afuwar yan Najeriya kan yawan katsewar wutar lantarki da ake fuskanta a baya-bayan nan tana mai amincewa da irin wahalar da hakan ta jefa gidaje da harkokin tattalin arziki.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, a daidai lokacin da jama’a ke ƙara nuna damuwa kan rashin tabbas a samar da wutar lantarki, wanda zafin rana ya ƙara tsananta shi.
A cewarsa, “Ina so na nemi afuwar yan Najeriya bisa wannan matsala ta wucin gadi da ke haddasa wahala, musamman a wannan lokaci na zafi mai tsanani.”
Ya ƙara da cewa matsalar ta shafi harkokin kasuwanci, makarantu da masana’antu, duk da cewa ba haka gwamnati ke so ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa ana ɗaukar matakai domin gyara lamarin, yana mai cewa cikin makonni biyu masu zuwa ana sa ran fara ganin sauyi a samar da wutar lantarki, sakamakon gyaran bututun iskar gas da kuma haɗin gwiwa da masu samar da gas.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kafa wani kwamiti na musamman domin sa ido kan yadda kamfanonin gas ke cika alƙawurransu na samar da iskar gas a cikin gida, yana mai jaddada cewa ƙarancin gas na daga cikin manyan matsalolin da ke hana samar da isashashiyar wutar lantarki a ƙasar.