Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaDuk jami’an gwamnati dake son tsayawa takara ya ajiye mukamun sa –...

Duk jami’an gwamnati dake son tsayawa takara ya ajiye mukamun sa – Gwamna Abba

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarni ga jami’anta masu niyyar shiga zabe su yi murabus daga mukamansu.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce umarnin ya fito ne ta hannun Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.

Sanarwar ta jaddada cewa matakin ya yi daidai da sashe na 88 karamin layi na 1 na dokar zabe ta 2026, wanda ya kayyade yadda jami’an gwamnati ke shiga harkokin siyasa.

Takardar Sanarwar ta rawaito Sakataren gwamnatin na cewa e an dauki matakin ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma samar da damar fafatawa ga dukkan masu neman mukamai.

Sanarwar dai na umartar dukkan masu ruwa da tsakin da abun ya shafa, da su tabbatar da bin umarnin, inda aka bukaci masu niyyar tsayawa takarar su yi murabus kafin ranar 31 ga Maris, 2026.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments