Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeRasha ta yi wa Ukraine luguden wuta cikin dare

Rasha ta yi wa Ukraine luguden wuta cikin dare

Ƙasar Rasha ta sake yi wa Ukraine luguden hare-haren da manyan makamai a ciki dare.

Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko ya ce an kai wa gundumomi da dama na birnin hare-haren bama-bamai.

Mista Klitschko ya kuma ce harin ya shafi gidaje da wata cibiyar kasuwanci da kuma wani asibiti.

Magajin garin ya ƙara da cewa an kashe mutum huɗu, sannan wasu 19 suka jikkata.

A halin da ake ciki, hukumomi a yankin Lviv da ke yamacin ƙasar sun ce an lalata muhimman ababen more rayuwa da dama.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments