Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soki ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, yana mai cewa ba su nuna ƙarfin siyasar da za su iya kalubalantarsa a zaɓen 2027 ba.
Tinubu ya ce jam’iyyun adawa sun takaita kamfen ɗinsu ne a kafafen sada zumunta, musamman Facebook, yayin da jam’iyyar APC ke gudanar da gangamin neman goyon baya a sassan ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Tinubu wajen bayyana waɗannan kalamai a ranar Laraba, yayin wani gangamin kamfen ɗin APC a filin wasa na Akure Township da ke Jihar Ondo.
Tinubu ya yi zargin cewa Atiku ya kasa samun goyon bayan tsofaffin gwamnonin Jihar Adamawa da sauran manyan ’yan siyasa a jihar, yana mai cewa hakan na nuna raunin tasirinsa a siyasar yankin.
Ya kuma soki Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra, inda ya yi iƙirarin cewa ba shi da wasu muhimman nasarorin da zai iya nunawa a matsayin hujjar neman shugabancin ƙasa.
Shugaban ƙasar ya bayyana gamsuwarsa da yadda jama’a suka halarci gangamin APC a wasu jihohi, ciki har da Kaduna, Cross River, Nasarawa, Ekiti, Akwa Ibom, Rivers da Ebonyi.
Ya buƙaci shugabannin APC a Ondo su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su haɗa kai domin tunkarar zaɓen 2027. Ya kuma ce jihar, wadda ke da masu rajistar zaɓe miliyan 2.1, ya kamata ta samar wa APC aƙalla ƙuri’u miliyan 1.2.
Tinubu ya umarci Gwamna Lucky Aiyedatiwa, wanda ke jagorantar kamfen ɗinsa a jihar, da ya buɗe ƙofarsa ga dukkan shugabannin jam’iyyar domin ba su damar bayar da gudummawa.
Tun da farko, shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce Jihar Ondo tana da ministoci uku a gwamnatin tarayya, wato Taiwo Oyedele, Bunmi Tunji-Ojo da Ayodele Olawande, inda ya buƙaci al’ummar jihar su nuna godiya ta hanyar zaɓen Tinubu a 2027.
A nasa jawabin, Gwamna Aiyedatiwa ya sake jaddada aniyar jihar na samar wa Tinubu ƙuri’u miliyan ɗaya, tare da gode masa kan manufofin da ya ce sun kawo sauyi a ƙasar.