Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiLabaraiHisba ta haramta wa ‘yan mata talla da daddare a Jihar Katsina

Hisba ta haramta wa ‘yan mata talla da daddare a Jihar Katsina

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta haramta wa ’yan mata gudanar da sana’ar talla da daddare a faɗin jihar, inda ta umurce su da dakatar da ayyukansu kafin ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ne ya bayyana matakin a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar.

Kwamandan ya bayyana cewa umarnin ya shafi ’yan matan da ke gudanar da sana’ar talla a jihar, inda ya ce dole ne su kammala ayyukansu kafin lokacin da hukumar ta kayyade.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments