Rikicin shugabanci da ya dabaibaye ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ya ƙara tsananta, bayan wani zaman sulhu da sarakunan gargajiya da shugabannin ƙungiyar suka gudanar an Abuja ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Taron wanda aka gudanar a ranar Talata a gidan mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da ke Maitama, ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu. Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa zaman ya tashi cikin tsaiko, ba tare da samun wata mafita kan rikicin ba.
Daga cikin sarakunan da suka halarci taron akwai Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da Aku Uka na Wukari, Dr. Manu Ishaku Adda Ali. Sai dai Sarkin Musulmi bai halarci taron ba, saboda wasu muhimman al’amuran ƙasa da yake gudanarwa.
Majiyoyi sun ce sarakunan sun nuna damuwarsu kan yadda kwamitin amintattu (BoT) da kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) suka kasa haɗa kai domin nemo mafita ga matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar Arewa.