Thursday, November 12, 2026
HomeKasashen wajeAna fargabar guguwar El Niño za ta sake haddasa mummunar ambaliya a...

Ana fargabar guguwar El Niño za ta sake haddasa mummunar ambaliya a Kenya

Wata mata mai suna Agnes Shikoli, mai shekara 62, da ke zaune a unguwar Kibera a birnin Nairobi na Kenya, ta bayyana fargabar sake afkuwar mummunar ambaliyar ruwa sakamakon hasashen samun ruwan sama mai yawa.

Wata mata mai suna Agnes Shikoli, mai shekara 62, da ke zaune a unguwar Kibera a birnin Nairobi na Kenya, ta bayyana fargabar sake afkuwar mummunar ambaliyar ruwa sakamakon hasashen samun ruwan sama mai yawa.

Shikoli ta shaida wa BBC cewa har yanzu tana cikin damuwa kan ambaliyar da ta afku a watan Maris, wadda ta yi sanadin mutuwar ƙanwarta Beatrice Khalayi mai shekara 58, tare da lalata gidaje da dama.

Ta ce ruwan ya kai tsakiyar bangon gidanta da ke kusa da kogin Ngong, har ma ya lalata wasu kayayyakinta. Mutuwar ƙanwarta kuma ta girgiza ta matuƙa.

Shikoli ta ce tana fargabar cewa sabon ruwan sama mai ƙarfi zai iya jawo rugujewar gidaje ko kuma ambaliyar ta yi sanadin mutuwar wasu mazauna yankin.

Wannan fargaba ta ƙaru ne yayin da ake hasashen samun guguwar El Niño mai ƙarfi, wadda masana yanayi ke cewa za ta iya haddasa matsanancin yanayi a sassa daban-daban na duniya.

A Kenya, ana fargabar cewa za a samu ruwan sama fiye da yadda aka saba, lamarin da ka iya sake haddasa ambaliya.

Hukumomi a Nairobi sun ƙara ƙaimi wajen tsaftace koguna da magudanan ruwa domin rage haɗarin ambaliya. A unguwar Kibera, ma’aikata ƙarƙashin shirin Climate Worx na ofishin Shugaban ƙasar, William Ruto, na kwashe shara da tarkacen da suka taru a kogin Ngong.

An ƙara yawan wannan aiki tun watan Agusta, bayan masana hasashen yanayi sun yi gargaɗin yiwuwar samun mummunan yanayi. Sai dai ma’aikatan na fuskantar ƙalubale saboda yawan tarkacen da suka toshe magudanan ruwa.

Shugaban hukumar kula da bala’o’i ta jihar Nairobi, Bramwell Simiyu, ya shaida wa BBC cewa rashin kula da magudanan ruwa tsawon shekaru na daga cikin dalilan asarar rayuka a ambaliyar farkon shekarar.

Ya ce kwashe tarkacen da suka toshe magudanan zai taimaka wajen rage haɗarin ambaliya da kuma ceton rayukan jama’a.

Unguwanni masu ƙaramin ƙarfi, musamman waɗanda ke kusa da koguna kamar Kibera da Mathare, na cikin waɗanda suka fi fuskantar barazanar ambaliya.

A irin waɗannan yankuna, gidaje da dama na kusa da bakin koguna, yayin da wasu aka gina su a gangaren da ke gefensu, lamarin da ke ƙara haɗarin rugujewa ko kwashe su idan aka samu ambaliya.

Simiyu ya ce tsarin magudanan ruwan Nairobi an tsara shi ne kimanin shekaru 30 da suka gabata, lokacin da birnin ke da al’umma kusan miliyan 2.5.

Amma yanzu, a cewarsa, yawan mutanen birnin ya kai kusan miliyan bakwai da rana da miliyan 5.5 da daddare.

Ya ƙara da cewa ana buƙatar dala miliyan 192 domin sake gina da inganta tsarin magudanan ruwa da na zubar da shara.

Sai dai har yanzu babu tabbacin cewa gwamnatin Kenya ko ƙaramar hukumar Nairobi za su iya samar da wannan kuɗi saboda matsalolin ƙarancin kuɗaɗe.

Wani shirin gwamnati mai suna Nairobi River Basin Regeneration Programme ya gano cewa gine-gine a kusa da koguna da rashin bin dokokin gine-gine na ƙara haɗarin ambaliya.

Shirin ya ba da shawarar samar da yankunan kariya a gefen koguna da kuma mayar da mutanen da ke cikin haɗari zuwa wuraren da suka fi aminci.

Simiyu ya yi hasashen cewa a yanayin da ambaliyar za ta fi tsanani, kusan mutane 100,000 da ke zaune a unguwannin masu ƙaramin ƙarfi za su iya fuskantar barazana.

A hasashen matsakaicin haɗari kuma, gidaje 5,000 da ke ɗauke da kusan mutane 20,000 na iya shiga cikin haɗari.

Hukumar hasashen yanayi ta Kenya ta ce daminar ƙarshen shekara kan fara ne daga Oktoba zuwa Disamba, inda watan Nuwamba ya fi samun ruwan sama mai yawa.

A wani hasashen da hukumar raya yankin gabashin Afirka ta IGAD ta fitar a watan Satumba, ta ce akwai yiwuwar kashi 81 cikin 100 na samun El Niño mai tsananin ƙarfi tsakanin Oktoba da Disambar 2026.

Masana sun kwatanta El Niño ta bana da wadda aka samu a shekarun 1997 zuwa 1998, wadda ta haddasa mummunar ambaliya a Kenya da Somalia.

Wata mai hasashen yanayi, Jemima Gacheru, ta shaida wa BBC cewa kamanceceniyar yanayin zafin ruwan tekun Indiya a waɗannan lokuta na iya haifar da ruwan sama mai tsanani.

Ta kuma bayyana cewa ban da El Niño a tekun Pasifik, akwai wani yanayin sauyin zafin ruwan teku da ake kira Indian Ocean Dipole, wanda ake sa ran zai ƙara kawo ruwan sama mai yawa a wasu sassan Kenya.

Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kusan mutane 900,000 a Kenya na iya rasa matsugunansu a bana, galibi sakamakon ambaliyar ruwan da ake hasashen za a samu.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments