Friday, November 13, 2026
HomeLabaraiZa a kaddamar da sabon littafi kan rayuwar Muhammadu Buhari da mulkinsa

Za a kaddamar da sabon littafi kan rayuwar Muhammadu Buhari da mulkinsa

Za a gabatar da sabon littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ga jama’a a ranar 19 ga watan Nuwamba a Abuja, inda littafin zai kunshi kundin tarihi guda uku da suka yi bayani kan rayuwarsa, aikin soja da kuma shugabancinsa na tsawon shekaru takwas.

Littafin mai suna The Making of Muhammadu Buhari: The Authorised Biography, wani masani kuma mai bincike mai suna Udo Yakubu ne ya rubuta shi, yayin da kamfanin May Publishing Limited ya wallafa shi.

Da yake magana a wani taron manema labarai, Yakubu ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana gudanar da bincike, tattaunawa da mutane da kuma tattara bayanai kafin kammala littafin.

Ya bayyana cewa littafin ya fara ne daga tarihin yarintar Buhari a Daura ta jihar Katsina, rayuwarsa a aikin soja, shigarsa siyasa har zuwa zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2015.

A cewarsa, kundin farko ya yi bayani kan asalinsa da aikin soja, na biyu ya mayar da hankali kan mulkinsa daga 2015 zuwa 2023, yayin da na uku ya yi nazari kan nasarori da ƙalubalen da suka shafi tsaro, tattalin arziki da shugabancinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments