Thursday, November 12, 2026
HomeLabarai2027: INEC ka iya yanke matsaya kan rikicin shugabancin ADC mako mai...

2027: INEC ka iya yanke matsaya kan rikicin shugabancin ADC mako mai zuwa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na iya tattauna rikicin shugabancin jam’iyyar ADC a taronta na mako mai zuwa, bayan dawowar shugabanta daga wani aikin hukuma.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na iya tattauna rikicin shugabancin jam’iyyar ADC a taronta na mako mai zuwa, bayan dawowar shugabanta daga wani aikin hukuma.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Malam Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan. Haruna, wanda shi ne shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe (IVEC), ya ce har zuwa daren Talata hukumar ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun ba.

Ya ce INEC ta karɓi takardar ɗaukaka ƙara da ADC ta shigar, tare da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, amma ba ta samu Certified True Copy (CTC) ɗin ba.

Haruna ya bayyana cewa sai hukumar ta gudanar da taro kafin ta yanke matsaya. Ya ce ana sa ran shugaban INEC zai dawo ranar Lahadi, don haka akwai yiwuwar gudanar da taron a ranar Talata ko Alhamis na mako mai zuwa.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa ba za a ɗauki waɗannan ranaku a matsayin tabbatattu ba, domin har yanzu ba a tabbatar da lokacin taron ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments