Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiLabaraiHukumar EHCON ta yaba wa Iconic Open University bayan tantance shirin karatun...

Hukumar EHCON ta yaba wa Iconic Open University bayan tantance shirin karatun Public Health

Hukumar Kula da Sana’ar Kiwon Lafiyar Muhalli ta Ƙasa (EHCON) ta gudanar da aikin tantance shirin karatun Kiwon Lafiya (Public Health) a Jami’ar Iconic Open University, inda ta yaba da tsarin da koyo da koyarwa na jami’ar.

A yayin tantancewar, tawagar hukumar ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Magatakardar EHCON, Mohammed Aminu M. ta bayyana gamsuwarta da yadda jami’ar ta tanadi kayan koyarwa, kayayyakin aiki da ƙwararrun ma’aikata domin gudanar da shirin karatun.

Mohammed Aminu M. ya bayyana cewa jami’ar ta yi fice a cikin cibiyoyin ilimi da hukumar ta ziyarta, yana mai cewa tsarin koyarwa da koyo na jami’ar ya burge tawagar sosai.

Ya ce: “A yayin gudanar da ayyukanmu, mun ziyarci cibiyoyin ilimi da dama, amma dole ne in bayyana cewa Iconic Open University ta bambanta. Wannan shi ne aikin tantancewa mafi kyau da muka gudanar zuwa yanzu. Tsarin koyon da jami’ar ke amfani da shi yana daga cikin mafi kyau.”

Tawagar ta gudanar da bincike kan kayan aikin jami’ar, tsarin karatu, ƙwarewar malamai da sauran matakan koyarwa domin tabbatar da cewa sun dace da ƙa’idojin ƙwararru da ake buƙata wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiyar muhalli da lafiyar al’umma a Najeriya.

Mataimakin magatakardar ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ba jami’ar goyon baya a shirye-shiryen karatun digiri na farko da na gaba, tare da yabawa mahukuntan jami’ar bisa jajircewarsu wajen samar da ingantaccen ilimi mai sauƙin samu.

Bisa ga sakamakon aikin tantancewar, ɗaliban da suka kammala karatun za su samu damar yin rijistar ƙwararru da kuma jarabawar lasisin aiki da EHCON ke gudanarwa, domin samun damar yin aikin kiwon lafiyar al’umma a Najeriya da sauran wurare.

Wannan nasara na zuwa ne bayan Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta ba Iconic Open University cikakken lasisin gudanar da ayyukanta a matsayin jami’a, bayan kammala wa’adin lasisin wucin gadi na gwaji.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments