Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiLabaraiNiMet ta yi hasashen samun hazo a Kano da wasu Jihohin Arewa

NiMet ta yi hasashen samun hazo a Kano da wasu Jihohin Arewa

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun hazo a wasu jihohin Arewa, ciki har da Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto a ranar Litinin.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin hasashen yanayin da ta fitar ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, a Abuja, inda ta ce ana sa ran samun yanayin rana a jihohin Arewa maso Gabas.

NiMet ta kuma yi hasashen cewa za a ci gaba da samun rana da hazo a wasu sassan Arewa a ranakun Talata da Laraba, yayin da ake sa ran samun tsawa da ruwan sama a kudancin Jihar Taraba ranar Talata da wasu sassan Jihar Kwara ranar Laraba.

Hukumar ta shawarci masu fama da cutar asma da sauran matsalolin numfashi da su ɗauki matakan kariya daga ƙura domin kauce wa matsalolin lafiya.

Haka kuma, ta gargaɗi jama’a da su guji fakewa ko tsayawa ƙarƙashin dogayen bishiyoyi a lokacin hadari, tare da cire na’urorin lantarki daga soket domin kauce wa haɗarin wutar lantarki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments