Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano za kuduri aniyar biya bashin ’yan fansho zuwa Afrilu 2027

Gwamnatin Kano za kuduri aniyar biya bashin ’yan fansho zuwa Afrilu 2027

Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin biyan dukkan bashin kuɗaɗen fansho da ta gada, da kuma waɗanda suka taru daga shekarar 2019 zuwa yanzu, wanda yawansu ya kai Naira biliyan 42.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar jihar karo na 42, wanda aka gudanar daga tsakar daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da biyan haƙƙin tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka shafe lokaci suna jiran kuɗaɗensu, tare da sauke nauyin bashin da ta gada.

Ya ƙara da cewa shirin biyan kuɗaɗen zai fara ne daga watan Nuwamba na wannan shekara zuwa ƙarshen watan Afrilu na shekara mai zuwa, wanda ke nufin za a kammala biyan bashin wata guda kafin cikar wa’adin mulkin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na farko.

Gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyarta ta biyan dukkan kuɗaɗen fanshon da ake bin ta, domin tabbatar da walwalar tsofaffin ma’aikata da kuma ba su haƙƙoƙinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments