Gwamnatin Tarayya ta nemi a dawo da shingayen bincike a manyan titunan Najeriya, tana mai cewa amfani da fasahar zamani zai iya mayar da su muhimman wuraren sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa da yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Leah Katung-Babatunde, ta fitar.
Ministan ya bayyana cewa amfani da fasahar zamani wajen gudanar da binciken zai bai wa jami’an tsaro damar tattara bayanan rajistar motoci da kuma sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa a manyan hanyoyin da ke haɗa jihohin ƙasar.
Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen gano mutanen da ake zargi da aikata laifuka, tare da ƙarfafa matakan tsaro a manyan hanyoyin ƙasar.