Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiLabaraiMai kwazo ba zai rasa abinci a Najeriya ba – Yari

Mai kwazo ba zai rasa abinci a Najeriya ba – Yari

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa duk ɗan Najeriya mai ƙwazo ya kamata ya iya samun abinci a kan teburinsa, duba da cewa ana samun kayan abinci a kasuwanni.

Yari ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wani gangamin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027, wanda aka gudanar a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Ya amince cewa akwai yunwa a Najeriya, amma ya yi tambaya kan ko akwai mutanen da suka je kasuwa da kuɗi suka kasa samun shinkafa ko wasu kayan abinci.

A cewarsa, kasancewar kayan abinci a kasuwanni na nufin cewa duk wanda yake da kuɗi zai iya sayen abin da zai ci.

Kalaman Yari na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan abinci da matsin tattalin arziki.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya zargi gwamnatocin baya da ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar. Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki kalaman shugaban, yana mai cewa manufofin gwamnatin Tinubu ne suka ƙara tsananta matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke ciki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments