Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiLabaraiINEC ta bayyana dalilin da ya sa ba ta cire sunan Atiku...

INEC ta bayyana dalilin da ya sa ba ta cire sunan Atiku daga takarar 2027 ba

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu kwafin hukuncin kotu ingantacce ba, wanda ya rushe shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin David Mark tare da soke zaɓen ’yan takarar da jam’iyyar ta fitar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu kwafin hukuncin kotu ingantacce ba, wanda ya rushe shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin David Mark tare da soke zaɓen ’yan takarar da jam’iyyar ta fitar.

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa INEC ta cire sunan Atiku Abubakar da mataimakinsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta.

Sai dai kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin ba, kuma ba ta tattauna batun ba.

Ya bayyana cewa samun kwafin hukuncin kotu na iya ɗaukar lokaci, don haka ba za a sa ran hukumar ta ɗauki mataki kan hukuncin da ba ta karɓa a hukumance ba.

Wani bincike da Daily Trust ta gudanar a shafin INEC ranar Juma’a ya nuna cewa har yanzu sunayen Atiku da Amaechi na nan a jerin ’yan takarar.

A ranar Alhamis ne Mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark da matakan da ya ɗauka, ciki har da tsayar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ADC na Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar shugabancin Mark.

Sai dai ADC da Atiku sun yi watsi da hukuncin, inda suka bayyana aniyarsu ta ɗaukaka ƙara tare da jaddada cewa za su ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments