Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa burinsa na sake lashe zaɓen gwamna a shekarar 2027 ba wani abu ne da zai sa ya yi komai domin cimma shi ba, yana mai cewa ba ya ɗaukar batun komawa kan mulki a matsayin dole.
Gwamnan ya jaddada cewa Allah ne ke bayar da mulki, kuma shi ne ke karɓewa a lokacin da ya so, don haka bai kamata mutum ya ɗauki mulki a matsayin abin da ba zai iya rayuwa ba tare da shi ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Abba ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin bikin rantsar da sababbin kwamishinoni biyu na gwamnatinsa.
Sababbin kwamishinonin su ne Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda aka naɗa a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai, da Balarabe Sa’idu Gani, wanda aka ba Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Hukumar Ma’adinai.