Friday, November 6, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun hallaka soja, da mata mai juna biyu da wasu...

’Yan bindiga sun hallaka soja, da mata mai juna biyu da wasu mutane 15 a Taraba

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani soja, mafarauci da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Sarkin Yamma, kusa da yankin Jeb-Jeb da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba.

Haka kuma, maharan sun ji wa wani soja rauni tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun kuma kai hari ƙauyen Ruwan Zafi, inda suka sace mutum 15, ciki har da mata da yara.

Harin ya faru ne a daren Talata, kwanaki 11 bayan wani hari da aka kai garin Binnari, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 60.

Wani jagoran al’umma a yankin, Tanko Bobbo Andami, ya ce mutum biyar sun kuɓuta bayan musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da mafarautan yankin a gefe guda, da maharan a gefe guda.

Ya ce maharan sun tsere zuwa daji tare da wasu daga cikin mutanen da suka sace.

Andami ya ƙara da cewa har yanzu mutum 15 na hannun masu garkuwa da mutane, inda ya yi kira ga gwamnatocin jihar Taraba da ta tarayya da su ƙara tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, bai amsa kiran da aka yi masa domin jin ta bakinsa kan lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments