Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa za ta ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa jinkirin kai kayayyakin zaɓe da aka fuskanta a wasu zaɓukan da suka gabata, yayin babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar ta kuma gargaɗi duk wanda ya yi barazana ko ya kai hari ga ma’aikatanta cewa zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin rangadin duba shirye-shiryen zaɓe a yankin Kudu maso Kudu, wanda ya kai shi Jihar Rivers.
A yayin rangadin, Amupitan ya kuma sanar da cewa hukumar ta rage adadin masu zaɓen da ake buƙata a rumfar zaɓe kafin a tura ƙarin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS, daga 1,250 zuwa 850.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin hukumar na inganta gudanar da zaɓe da kuma tabbatar da cewa masu zaɓe sun samu damar kaɗa ƙuri’unsu cikin sauƙi.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen zaɓen 2027, tare da tabbatar da tsaron ma’aikatanta da kayayyakin zaɓe domin gudanar da sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.