Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiSojoji sun ba jami’in da ya ƙi karbar cin hanci kyautar N500,000

Sojoji sun ba jami’in da ya ƙi karbar cin hanci kyautar N500,000

Rundunar sojin Najeriya ta ba wani soja mai suna Private Utim Terwase kyautar N500,000 bayan ya ƙi karɓar cin hancin da wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya ba shi.

Rundunar sojin Najeriya ta ba wani soja mai suna Private Utim Terwase kyautar N500,000 bayan ya ƙi karɓar cin hancin da wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya ba shi.

Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin tserewa bayan kama shi, inda ya miƙa wa sojan N500,000 domin ya sake shi.

Sai dai Terwase ya ƙi karɓar kuɗin, sannan ya miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace.

Kwamandan runduna ta uku ta sojin ƙasa, Manjo Janar Maxwell Dangana, ne ya bayar da kyautar ta hannun kwamandan sashe na shida, Kanal Philimon Malgwi.

Kakakin Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Chinonso Oteh, ya ce kwamandan ya yaba wa sojan bisa gaskiya da ƙwarewar aiki, yana mai cewa kyautar ta N500,000 na nuna godiya ga jajircewarsa da ƙin cin hancin da ya yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments