Gwamnatin Jihar Kebbi da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda shi ne ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, sun yi musayar zarge-zarge kan rushewar wani gidansa da ke kan titin Sani Abacha Bypass a Birnin Kebbi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta bayyana rushewar ginin a matsayin wani rikicin mallakar fili tsakanin wasu mutane, tana mai cewa lamarin ba shi da alaƙa da siyasa.
Sai dai Malami ya zargi abokan hamayyarsa na siyasa da hannu wajen rusa kadararsa, yana mai cewa an yi hakan ne domin tunzura shi da magoya bayansa.
Rahotannin sun nuna cewa ɓangarorin biyu sun gabatar da bayanai mabambanta kan dalilin rushewar ginin, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar.
Yayin da gwamnatin jihar ke danganta lamarin da rikicin mallakar fili, Malami na ganin akwai alaƙar siyasa a cikin abin da ya faru.