Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wani mai shekara 29 mai suna Emmanuel Olatonok, bisa zargin kashe wani mutum mai suna Ibrahim Shago, mai shekara 32, a yankin Rafin Sanyi da ke Ƙaramar Hukumar Dutse.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yammacin Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, bayan wani saɓani ya ɓarke tsakanin mutanen biyu.
A cewar rundunar, wanda ake zargin mai aski ne a Moonlight Hotel da ke Rafin Sanyi, ya caka wa marigayin wuƙa a wuya a lokacin takaddamar. An kuma zarge shi da kasancewa cikin maye a lokacin faruwar lamarin.
An garzaya da Shago, wanda mazaunin garin Karnaya ne, zuwa asibiti domin samun kulawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa. Bayan faruwar lamarin, wasu matasa sun taru a wurin tare da yunƙurin lalata otal ɗin.
Sai dai jami’an ’yan sanda daga sashen Dutse sun shiga tsakani tare da shawo kan lamarin. Rundunar ta ce wanda ake zargin yana hannunta, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ’yan sanda, CP Tijjani Murtala, ya yi kira ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.