Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaEl-Rufai ya umarci magoya bayansa su zaɓi ADC a dukkan matakai a...

El-Rufai ya umarci magoya bayansa su zaɓi ADC a dukkan matakai a zaɓen 2027

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci magoya bayansa da su zaɓi jam’iyyar ADC a dukkan matakai a babban zaɓen shekarar 2027.

Mataimakiyar Shugabar ADC ta Ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Hafsat Baba, ce ta bayyana hakan, inda ta ce El-Rufai ya kuma buƙaci magoya bayansa su kasance cikin haɗin kai, zaman lafiya da bin doka da oda domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a Jihar Kaduna.

Hafsat Baba ta bayyana hakan ne yayin wani taron ƙungiyoyin magoya bayan tsohon gwamnan da aka gudanar a Kaduna, wanda ta ce an shirya shi ne domin haɗa kan ƙungiyoyin da kuma daidaita ayyukansu gabanin zaɓen 2027.

A cewarta, El-Rufai ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin magoya bayansa, yana mai cewa haɗin kansu ne zai taimaka musu wajen cimma manufofinsu a lokacin zaɓe.

Ta ce saƙon tsohon gwamnan a bayyane yake, inda ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ADC a zaɓen shugaban ƙasa, na gwamna, Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dokokin Jiha.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments