Friday, November 6, 2026
HomeTsaroNDLEA ta kama mata da harsasan AK-47 guda 266 a Kaduna

NDLEA ta kama mata da harsasan AK-47 guda 266 a Kaduna

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata mai suna Aisha Isah da harsasan bindigar AK-47 guda 266 a wurin karɓar kuɗin hanya na Kaduna Toll Gate, da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Jami’in Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar reshen Jihar Kaduna, S. Garba ASN, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce jami’an hukumar sun kama matar ne yayin gudanar da ayyukansu a yankin.

A wani samame na daban da jami’an NDLEA suka gudanar a yankin Banke da ke Jihar Kaduna, sun kuma cafke mutane bakwai tare da ƙwato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 178.85.

Hukumar ta kuma ƙwato wasu ƙwayoyi da suka haɗa da Diazepam, Tramadol, Exol 5 da Pregabalin a yayin samamen.

Shugaban NDLEA na Jihar Kaduna, CN Maijama’a Muhammad, ya buƙaci jami’an hukumar da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke da alaƙa da su a jihar.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukanta domin dakile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma tabbatar da tsaro a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments