Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanarwa a faɗin Najeriya za su sa ya yi wuya jam’iyyun adawa su kayar da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wike ya ce ayyukan samar da ababen more rayuwa da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun bai wa jam’iyyar APC damar gabatar da nasarorinta ga ’yan Najeriya yayin yaƙin neman zaɓe.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, bayan duba wasu ayyukan tituna da ake gudanarwa a Abuja, inda ya ce mazauna babban birnin tarayya sun shaida ci gaba a fannin samar da ababen more rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Ya ƙara da cewa waɗannan ayyuka za su kasance cikin abubuwan da APC za ta yi amfani da su wajen neman goyon bayan masu zaɓe gabanin babban zaɓen ƙasar da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027.
A yayin ziyarar, Wike ya duba ayyukan titin Inner Southern Expressway, Southern Parkway da sauran ayyukan hanyoyi a gundumar Kaura, domin tantance yadda ake gudanar da su da kuma ko ana bin jadawalin lokacin kammalawa.
Ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da aka samu, inda ya ce an tsara kammala manyan ayyuka guda biyu tare da miƙa su a watan Disamba.
Ya kuma ce kamfanin da ke gudanar da wani aikin ya tabbatar masa cewa zai kammala shi kafin ranar 15 ga Disamba.
Wike ya ce gwamnati ta sanya wa kanta wa’adin kammala manyan ayyukan more rayuwa kafin zaɓe, kuma tana aiki tuƙuru domin cimma wannan buri.