Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiNajeriya na fuskantar rabuwar kai, dole mu tashi mu yaki hakan –...

Najeriya na fuskantar rabuwar kai, dole mu tashi mu yaki hakan – Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin haɗa kan ’yan Najeriya, magance matsalar rashin tsaro da kuma fitar da miliyoyin jama’a daga talauci idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa da magoya bayansa a Jos, babban birnin Jihar Plateau.

A yayin taron, tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar rarrabuwar kai tsakanin al’ummomi, yana mai cewa akwai buƙatar ’yan ƙasar su tashi tsaye domin yaƙi da matsalar.

Obi ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa, samar da tsaro, bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da shugabanci na gari.

Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar matakan da za su taimaka wajen rage talauci da inganta rayuwar miliyoyin ’yan Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments