Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiMaguɗin zaɓe ba ya faruwa a ranar zaɓe kaɗai – Umar Gurama

Maguɗin zaɓe ba ya faruwa a ranar zaɓe kaɗai – Umar Gurama

Tsohon ma’aikacin gwamnati kuma ɗan siyasa daga Gombe, Malam Umar Gurama, ya ce ana iya yin maguɗin zaɓe tun kafin ranar kaɗa ƙuri’a, ta hanyar hana jam’iyyun adawa gudanar da harkokinsu.

Tsohon ma’aikacin gwamnati kuma ɗan siyasa daga Gombe, Malam Umar Gurama, ya ce ana iya yin maguɗin zaɓe tun kafin ranar kaɗa ƙuri’a, ta hanyar hana jam’iyyun adawa gudanar da harkokinsu.

Ya ce hana ’yan adawa amfani da wuraren taro, cire kayan kamfen da takaita musu damar yaɗa saƙonsu duk wasu hanyoyi ne na raunana su. Ya kawo misalin lokacin da Muhammadu Buhari ke takarar shugaban ƙasa, inda aka zargi wani gwamna da hana shi amfani da filin wasa na Gombe.

Gurama ya ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta biyu suna gudanar da ayyukansu cikin ’yanci, amma a yanzu da dama ba sa aiki yadda ya kamata. Ya ce hakan na raunana dimokuraɗiyya, domin mambobin jam’iyyu da dama ba su san manufofi da kundin tsarin jam’iyyunsu ba.

Ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da amfani da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun adawa wajen raunana su, ta hanyar ƙarfafa wasu mambobi su garzaya kotu. Ya yi gargaɗin cewa raunana adawa na iya haifar da mulkin kama-karya.

Ya shawarci jam’iyyun adawa su kasance masu jajircewa tare da kare tsarinsu daga rarrabuwar kai. Haka kuma, ya bukaci a yi gyare-gyare a hukumomin gwamnati domin tabbatar da kare haƙƙoƙin ’yan Najeriya da kundin tsarin mulki ya ba su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments